Al Sisi ya bayayna cewa, bisa la’akari ad canjin da aka samu a duniya, ya zama wajibi akan musulmi musamman ma malamai su mayar da hankali matuka ga farmakin da ake kai wa muslunci ko ta ina, musamman a shafukan yanar gizo.
Shugaban ya ce da dama daga cikin masu akidar kin jinin musulunci suna yada akidojinsu ne ta hanyar shafukan sadarwa, kuma hakan ya kan yi tasiria a cikin zukatan mutanen da ba su san addinin muslunci, wanda kuam nauyi kan malamai su ma su bayyana hakikanin koyarwa ta zaman lafiya da tausayi da ‘yan adamtaka irin ta addinin muslunci.
A jiya ne aka kammala zaman taro na malamai mambobi a cibiyar fatawa ta Azhar wadda take da rassa a kasashen duniya daban-daban, inda malamai mambobi wannan cibiya da suke wakiltar Azhar suka taru domin tattauna hanyoyi karfafa fatawoyi an addinin muslunci, wanda shugaban ya samu halarta.
A wani labarin na daban isra’ila ta fara nuna damuwa game da bangado leken asirin da ake zargin kamfanin NSO na kasar da hannu a ciki.
A halin da ake ciki dai Isra’ilar ta kafa wani kwamitin bincike domin bin diddigin lamarin, bisa fargabar kada hakan ya janyo mata rikicin diflomatsiyya.
Ministan tsaron kasar Benny Gantz, ya ce sunan nan suna duba batun.
A kwanan nan ne dai aka bankado labarin leken asirin da ake zargin kamfanin Isra’ila mai leken asiri na NSO da kuma Pegasus.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron da Shugaban kasar Iraki Barham Saleh da na cikin mutane dubu 50 da ake zargin an yi wa leken asiri da manhajar ta Pegasus.