Shugaban Majalisar Tarayyar Turai Zai Tattauna Da Kasar Qatar Kan Matsalar Makamashi.
Rahotanni sun bayyana cewa a gobe Talata ce shugaban majalisar kungiyar tarayyar Turai Charles Michel zai kai ziyara birnin Doha na kasar Qatar kuma zai tattaunawa da mahukumtan kasar kan batun matsalar makamashi da kasashen kungiyar ke fuskanta adaidai lokacin da take neman wani zabi game da iskar Gas da suke saya daga kasar rasha,tun bayan barkewar yaki tsakanin ta da kasar Ukrain a watan fabareru da ya gabata.
Kasar Qatar a matsayinta na daya daga cikin manyan kasashen duniya dake fitar da Iskar Gas tana tattaunawa da masu sayan Gas a kasashen turai da dama sai dai har yanzu ba’a sanar da kulla wata yarjejeniya akan lamarin ba.
Charles Michel zai gana da manayan jami’an gwamatin kasar domin sake bitan muhimman batutuwa da suka shafi yankin da ma na kasa da kasa da suka hada da yakin Rasha da Ukrain, matsalar makamashi, da kuma batun kasar Afghanistan, Iran, da rikicin Isara’ila da falasdinawa.
Kasar Qatar na neman sabbin kwastomomi don fadada yawan iskar gas din da take fitawa da hakan zai kara bunkasa yawan kayayyakin da take fitarwa zuwa kusan kashi 63 % kuma ana shirin shigar da shi a hanyar yanar gozi a farkon shekara ta 2027.