Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na – ABNA – ya kawo maku cigaban bayanin shugaban majalisar Ahlul-Bait AS ta duniya dangane da ziyarar da ya ka kasashen gabashin Afirka:
Abna: Ganin cewa an yi taruruka da zama daban-daban a Afirka; zaku iya Faɗa mani game da mafi mahimmancin nasarar da aka samu wajen gudanar da waɗannan tarurrukan.
Shugaban Majalisar Ahlul-Baiti (AS) Ta Duniya: Tafiya zuwa Afirka tare da tarukan da Majalisar ta shirya wani muhimmin lamari ne domin a taron koli na bakwai da aka gudanar a kasar Iran a watan ugustan shekara ta 2022, an amince da cewa muna da tarukan yanki kuma za a gudanar da wani bangare na wadannan tarurrukan a yankin. Mun kuma jaddada cewa ya kamata waɗannan shirye-shiryen su kasance masu dacewa kuma kada su kasance kawai na zahiri da talla kamar wasu tarurruka.
Dole ne mu yi la’akari da manufofin gudanar da waɗannan tarurrukan kuma mu tsara hanyar bisa ga manufofi; A saboda haka ne muka kafa hedkwata a majalisar don duba yadda aka gudanar da taruka da majalisai daban-daban da kuma cimma nasarar da ake bukata.
A cikin duniyar yau, domin muna fuskantar abubuwa masu rikitarwa waɗanda dole ne a yi la’akari da su a cikin tsare-tsarenmu.
Duniyar zamani da bayan zamani, tare da alamomi da abubuwan da ke tattare da su, suna haifar da jerin batutuwa da sakamako, wanda ya zamo wasu mutane ne je tafiyar da duniya.
Muna adawa da tsarin haɗin kan duniya ga masu girman kai, amma dole ne mu yarda cewa “tafarkin shi ne tafarkin dunkulewar duniya”. Duniya ta yau ta sha bamban da ta shekaru 50 da suka gabata, kuma muna ganin abubuwa da dama da suka faru a fagage daban-daban, wasu kuma suna kokarin cin moriyar dukiyar duniya ta hanyoyi daban-daban da bin tafarkin mulkin mallaka.
A wannan zamani, wasu mutane sun yi niyya don su karkatar da matasa. Mulkin sassaucin ra’ayi a duniya yana bin ‘yancin kai na ɗabi’a, wanda ke neman yada lalata da bata. A cikin shekaru 13 ko 14 da na yi a Turai, ban ga abin da ya fito daga cikin kunshin karatunsu ba in ban da ilimin boko ko na zamani, ta yadda sabbin zamani ba za su mai da hankali ga addini da koyarwar addini ba; Suna neman tayar da tsararraki waɗanda ba ruwansu da ruhiyya sai su zabi ruhiyya mara nauyi sassauka.
Yanzu, a cikin Turai da Amurka, muna da kusan kirkirarun ruhohiyyoyi 4000 waɗanda ke da alhaki kula da wannan yanayi kuma suna ƙoƙarin canza wannan tunanin zuwa yanayin ilimi na matasa.
Game da mata, ana aiwatar da irin waɗannan tsare-tsare, Turawan Yamma suna ƙoƙarin karkatar da mata zuwa wata hanya’ idan ka kalli fina-finan da aka yi a Turai a cikin shekaru dari da suka wuce, za ka gane cewa hijabi da suturar mata a kasashen Turai ya zama tsirara, don haka a yau manyan kamfanoni suna amfani da mata a matsayin kayan aiki suna amfani da su don sayar da samfurorin kayayyakin su.
Na lura a wasu kasashen Turai cewa ana amfani da mata a matsayin talla a tagogin shaguna kuma ana daukar mata a matsayin kayan aikin sayar da kayayyaki daban-daban.
A sakamakon haka, a yau muna fuskantar barazana iri biyu, daya da ta shafi samari, daya kuma ga matan al’umma; gungun mata ya ƙunshi rabin al’ummar duniya, suna da girma mai yawa, don haka karkatar da yawan mata ana daukarsa a matsayin babbar barazana. Shugaban
Za mu ci gaba….
Source: ABNAHAUSA