Shugaban kungiyar kasashen Larabawa wanda yake birnin Alkahira na kasar Masar ya aikawa shugabannin kasar Libya yaso bayan da suke dage zaman shugaban kasa wanda yakamata a gudanar a cikin wannan wato zuwa wani lokacin da basu bayyana ba.
A cikin sakon dai Ahmed Aboul Gheit yay i kira ga shuwagabannin kasar su dubi al-ummar kasarsu da kuma matsalolin da suke ciki, kada su biyewa son zuciyarsu, su gaggauta gudanar da zabubbuka a kasar wanda zai taimaka wajen dawo da zaman lafiya mai dorewa a kasar.
Daga karshe Ahmed Aboul Gheit ya kirayi ‘yan siyasar kasar su warware matsalolin da ke tsakaninsu a cikin ruwan sanya ta hanyar tattaunawa, kada su dauki makamai don wani sabani da ya bullo tsakaninsu.