Shugaban kasar Koriya ta arewa ya haramta wa ‘yan kasar dariya ko nuna wata alamar farin ciki na tsawon kwana 11 a dukkan fadin kasar Wannan lamarin na zuwa ne domin makokin cikar mahaifinsa shekaru 10 da rasuwa wanda ya mulki kasar na tsawon shekaru 17 An umarci ‘yan sanda da su hana jama’a nuna alamar farin ciki kama daga shan giya, a ranar 17 ga wata kuwa, har cefane an haramta zuwa yin shi A cikin kwanakin,
ko da kuwa mutuwa aka yi a kowanne gida, ba a yarda a yi kuka mai sauti ba kuma ba za a fitar da gawar ba sai bayan cikar makokin.
Koriya ta arewa – Shugaban kasar Koriya ta arewa, Kim Jong-un ya haramta wa ‘yan kasar sa nuna kowacce irin al’amari farin ciki na tsawon kwanaki 11 domin cikar shekaru 10 da rasuwar Kim Jong-Il.
Kamar yadda rahotannin The Telegraph suka bayyana, wannan alamun nuna farin cikin sun haramta a bayyana su kama daga dariya ko shan giya na tsawon kwanaki 11 domin makoki.
A ranar 17 ga watan Disamba kuwa, wacce ita ce ranar da Kim Jong-Il ya rasu, an haramta wa kowa zuwa cefane, Tribune Online ta ruwaito.
Kim Jong-il, wanda ya mulki masarautar daga 1994 har zuwa mutuwarsa a 2011 bayan kamuwa da ciwon zuciya a shekaru 69 da yayi a duniya, shi ne mahaifin shugaban kasar na yanzu, Kim Jong-un.
A zamanin mulkinsa ne aka fuskanci wani babban ibtila’i a kasar Koriya ta arewa, wata gagarumar yunwa da aka yi a shekarun tsakiyar 1990s wanda ake kira da ‘Arduous March’. Kiyasi ya nuna cewa, rayuka 3.5 miliyan ne suka salwanta a cikin shekaru hudu kacal. Kim Jong-II ya mulki kasar Koriya ta arewa na tsawon shekara 17 kafin mutuwarsa a shekarar 2011.
A kowacce shekara ake yin makokin mutuwar Kim Jong-II da mahaifinsa Kim II-sung a kasar. A kowacce shekara kuwa na tsawon kwanaki goma ake makokin amma an kara shekara daya ne wannan karon saboda cikarsu shekaru goma tun bayan mutuwar Kim Jong-II.
A wannan lokacin, ana bukatar ‘yan Koriya ta arewa da su yi kokarin ciyar da talakawa da masu neman abin ci. A halin yanzu, kasar Koriya ta arewa na fama da rashin abinci sakamakon annobar korona da aka yi, lamarin da yasa ake tsoron aukuwar Arduous March karo na biyu.
A wani labari na daban, shugaban Koriya ta arewa, Kim Jong-Un ya haramta wa duk wasu ‘yan kasar kwaikwayon irin salon sutturar da ya ke saka wa. Shugaban da gaske ya ke don ya umarci ‘yan sanda da yawata cikin kasar don kwace irin rigunan sanyinsa daga jama’a da masu shagunan da ke siyarwa.
Radio Free Asia sun ruwaito yadda aka haramta amfani da rigar sanyi ta fatar dabbobi don gudun kwafar salo irin na babban shugaban.