Shugaban Korea ta Arewa Kim Jong Un ya soki Amurka da zama ummul-haba-isin tashe-tashen hankulan da ke faruwa a tsibiri Korea, yayin da a gefe guda ya bayyana makwabciyarsu Korea ta Kudu a matsayin munafuka.
A ‘yan kwanakin nan Korea ta Arewa ta yi gwaje-gwajen manyan makamai masu linzami duk da takunkuman da kasashen duniya suka lafta mata saboda mallakar haramtattun makaman.
Duk da cewa gwamnatin shugaba Joe Biden na Amurka ta sha nanata cewa ba ta da niyyar muzguna wa Korea ta Arewa ko yaki da ita, Kim ya ce dabi’unta ba su ba shi hujjar amincewa da ita.
A wani labarin na daban a ranar Lahadi Koriya ta Arewa ta zargi shugaban Amurka Joe Biden da bin manufofin nuna kiyayya, tana mai watsi da abin da ta kira diflomasiyyar yaudara ta Amurka, inda ta yi gargadin mayar da martani a kan duk wani cin zali da za a yi mata.
A ranar Juma’a fadar White House ta ce a shirye shugaba Biden yake don tattaunawa da Koriya ta Arewa a kan batun jingine shirin nukiliyarta, biyo bayan kammala nazarin manufofi, amma Pyongyang ta mayar da martani tana cewa, Biden ya tafka babban kuskure.