Shugaban Kasar Rasha Ya Shaidawa Takwaransa Na Turkiya Shirinsa Na Tattaunawa Da Kasar Ukiraniya.
Shugaban kasar ta Rasha Vlademir Putin wanda ya zanta ta wayar tarho da takwaransa na kasar Turkiya Rajab Tayyib Urdugan, ya bayyana yadda harin sojan da kasarsa take kai wa a yankin Dunbass yake tafiya.
Vlademir Putin ya kuma shaidawa shugaba Urdugan ta Turkiya cewa; Kasarsa a shirye take ta tattauna da shugabannin Ukiraniya da kuma wasu kasashen, domin a kai ga samun mafita ta rikicin da ake yi.”
Sai dai shugaban kasar ta Rasha ya ce; Bata lokaci da mahukuntan kasar Ukiraniya suke yi akan tattaunawar ba zai yi musu amfani ba domin manufarsa samun damar da za su sake shiyar sojojinsu.
Bugu da kari,shugaban kasar Rasha ya ce Abu daya ne zai sa Rasha ta daina yaki, shi ne shugabannin Ukiraniya su daina gaba da Rasha, sannan kuma su aikata dukkanin sharuddan Moscow.
Bangarorin biyu na Rasha da Turkiya sun bayyana fatansu na ganin kasashensu sun cigaba da barin kofofin tuntubar juna a bude, ta hanyoyin ma’aikatun tsaro da kuma harkokin waje.