Shugaban Kasar Mauritaniya Ya Isa Saudiyya Domin Gudanar Da Aikin Hajji.
Shugaban kasar Mauritaniya Mohamed Ould Cheikh El-Ghazouani ya bar birnin Nouakchott zuwa kasar Saudiyya domin gudanar da aikin hajji.
Ghazwani zai fara ziyarar ne daga birnin Madina kafin ya wuce Makkah domin yin aikin Hajji, wanda zai fara ranar Alhamis mai zuwa 8 ga Zul-Hijja.
A baya dai shugaban na Mauritaniya ya kai ziyara kasar Saudiyya domin gudanar da aikin Umrah, yayin da wasu daga cikin manyan jami’an Saudiyya da suka hada da ministan harkokin wajen kasar suka ziyarci kasar ta Mauritania kwanakin baya.
READ MORE : Iran Da Venezuela Sun Jaddada Wajabcin Kara Karfafa Kawance Da Alakoki A Tsakaninsu.
Kafin tafiyar tasa, Ould Cheikh El-Ghazouani ya gayyaci firaministansa Mohamed Ould Bilal a jiya zuwa fadar shugaban kasa, kamar yadda wata majiya mai tushe a cikin gwamnatin Mauritania ta bayyana, inda ganawar tasu ta dauki sama da sa’a daya da rabi.
READ MORE : Tsohon Shugaban Burkina Blaise Compaoré Zai Koma Gida.
READ MORE : Aljeriya Ta Yi Wa Fursunoni 14,000 Ahuwa Albarkacin Ranar ‘Yanci.
READ MORE : ‘Yan Siyasa A Sudan Sun Yi Fatali Da Tayin Janar Al-Burhan.
READ MORE : Amurka; Dan Bindiga Ya Hallaka Mutum 6 Yayin Faretin Ranar ‘Yancin Kai.