Shugaban Kasar Jamus Ya yi Watsi Da Bukatar Amurka Da Ukrain Kan Siyan Gas Daga Rasha.
Dagangan ne kasashen turai suka cire batun siyan makamashi daga kasar Rasha daga cikin takunkumin da ta kakaba mata, Plaf Sholz shugaban kasar Jamusa a wata sanarwa da ya fitar yace a halin yanzu babu wata hanyar da kasahen turai za su iya samar da makamashi domin amfani das hi lokacin zafi da samar da wutar lantarki da masana’antu ba , don haka dole ne mu fi bada fifiko wajen yi wa alumma hidima da samar da abubuwan bukatar rayuwa ta yau da kullum ga alummarmu.
Kasar Ukrain da goyon bayan Amurka da wasu yan siyasar kasashen turai ta bukaci dole kasashen turai su dakatar da samar da makamashi daga kasar Rasha, sai dai sun ce lamari ne da zai yi wu a cikin dare daya ba.
READ MORE : Iran Ta Jaddada Aniyarta Ta Kokarin Samar Da Hadin Kai tsakanin Kasashen Musulmi.
Wannan yana zuwa ne bayan kalaman da sakataren harkokin wajen Amurka Antony blinkin yayi dake nuna cewa Amurka da saurankasasshen turai sun tattaunawa na ganin sun dakatar da shigo da man fetur daga kasar Rasha,
Daga karshe shugaban kasar Ukrain Voldymyr Zelenskky yayi kira da a kauracewa shigo da duk wani kaya daga rash musamman manfetur da iskar gasa da dangoginsu.