Shugaban kasar Iran ya Isa birnin Doha na kasar Qatar a ziyarar ta Musamman.
A yau ne shugaban kasar iran Ibrahim Ra’isi ya isa birnin Doha na kasar Qatar a wata ziyarar kwanaki biyu, bisa gayyatar da sarkin Qatar Tamin bin Hamd Al thani ya yi masa.
Kafin ya bar birnin Tehran Ibrahim Ra’isi ya yi Karin haske game da makasudin ziyarar ta sa ida ya nuna cewa wani mataki ne na kara karfafa dangantaka da kasashen yankin musamman ma kasashe dake kewayen tekun Fasha,
Ministan harkokn waje da na man fetru da na ala’adu da yawon bude ido suna daga cikin jami’an da suka rufa masa baya a ziyarar ta sa.
Daga cikin ziyarar ta sa shgaban iran zai halarci taron kungiyar kasashe masu fitar da iskar Gas karo na 6, kana ya gana da jami’an wasu kasashen da kuma yan kasuwa iraniyawa dake zaune a kasar
Shuwagabannin kasashen ne ke halartar taron tare da manyan jami’an gwamnati na kasashen dake fitar da iskar Gas , kuma wasu daga cikinsu zasu gana da shugaban kasar Iran agefen taron.