Shugaban Kasar Iran Ya Ce; Kasarsa A Shirye Take Ta Shiga Tsakanin Rasha Da Ukiraniya domin kawo karshen yaki.
Shugaban kasar ta Iran Sayyid Ibrahim Ra’isy ya bayyana hakan ne a yayin taron majalisar ministoci a jiya Lahari yana mai kara da cewa: Iran ta fahimci damuwa ta fuskar tsaro da Rasha take da shi akan kungiyar yarjejeniyar tsaro ta Nato na shekaru masu tsawo, sai dai duk da haka ta yi imani da ‘yancin dukkanin kasashen duniya.
Sayyid Ra’isy ya kuma ce; A shirye muke mu fitar da mafita ta diplomasiyya wacce za ta kai ga tabbatar da zaman lafiya.
Shugaban na kasar Iran ya kuma kara da cewa; Kare rayuka da dukiyoyi wani lamari ne da ya zama wajibi,bisa dokokin kasa da kasa da kuma ‘yan’adamtaka.
Danage da Daliban Iran da suke karatun a kasar ta Ukiraniya, shugaban kasar ta Iran ya bayar da umarnin daukar dukkanin matakan da suka dace domin ba su kariya da dawo da su gida.