Shugaban kasar wanda ya kasance babban bako a rana ta farko ta zama na 12 na majalisar kwararru ta jagoranci a zango na biyar, a jawabinsa a wannan zama ya taya murnar makon tsaro mai tsarki tare da jinjinawa shahidan da aka samu a lokacin wannan yakin…
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) – ABNA – ya habarta cewa, shugaban kasar Iran Ibrahim Raisi ya tabbatar da cewa gwamnatinsa tana da karfin magance matsalolin da ke addabar kasar, kuma idan gwamnatin ta samu nasara a fagen manufofin ketare, ya kasance bisa la’akari da bin umarnin Jagoran juyin juya halin Musulunci.
Shugaban kasar ya kasance babban bako a rana ta farko ta zama na 12 na majalisar kwararru ta jagoranci a zango na biyar, inda a jawabin da ya gabatar a wannan zama, ya taya murnar makon tsaro mai tsarki, tare da jinjinawa shahidan da aka rasa a yakin.Ya kuma taya murnar Makon Hadin Kai da zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa.
Shugaban kasar ya yi ishara da irin nasarorin da Jamhuriyar Musulunci ta samu, inda ya ce: A bangaren al’adu, siyasa da tattalin arziki, wadanda su ne manya kuma al’amurran da suka shafi kasar nan, yanayin da ake da shi yana da kyau ta yadda za a samar da dukkan karfin da al’umma za ta samu in da ya kai matsayin da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bukata daga garemu mu a matsayinmu na masu daukar nauyin wannan tsari, wajibi ne mu san abin da ya wajaba a yi a wadannan fagage, ko dai bisa bukatun kasa, ko kuma bisa kyawawan manufofinmu, kuma za mu iya
Don hakan zamu iya magance matsalolin kasarmu, domin a wurare ne da aka gwada aiwatar da umarnin Imam Khumaini da Jagoran juyin juya halin Musulunci kuma aka samu nasara muna ganin tasirin ci gaba, wuraren da hakan kuma bai faru ba, sai muka koma ga wasu batutuwa don magance matsalar.”
Raisi ya yi ishara da irin nasarorin da gwamnatinsa ta samu a fagen siyasar kasashen waje, inda ya ce: Idan har gwamnati mai ci ta samu wasu nasarori a fagen siyasar kasashen waje, to ta kasance bisa bin umarnin jagoran juyin juya halin Musulunci ne, idan kuwa aka samu wani matsala to wannan laifin mu ne”.
Ya jaddada cewa a fagen tattalin arziki, da a ce an bi manufar da jagoran juyin juya halin Musulunci ya tsara mai taken “Tattalin Arzikin gwagwarmaya”, da yanayin kasar ya sha bamban a yau, ya kuma kara da cewa. “A fagen al’adu da siyasa kuma shima da a ce an aiwatar da umarninsa da ra’ayoyinsa, da tabbas za mu sami yanayi mafi kyau fiye da halin da ake ciki a yanzu.”
A karshe ya yi ishara da ci gaban tattalin arzikin da kasar ta samu a lokacin gwamnatinsa inda ya ce: Ci gaban tattalin arzikin da aka samu ya samu ne sakamakon karuwar zuba jari da karuwar samar da kayayyaki da ya kai kashi 2.6 cikin 100 a bana, a cewar sanarwar da cibiyar kididdiga ta Iran ta fitar.
Wanda cibiyar Samar da Samfura ta sanar a yau cewa muna da haɓakar ƙarfin samarwa da kashi 3.5 cikin ɗari.”
Source LEADERSHIPHAUSA