Shugaban Kasar Faransa Ya Ce Rasha Tana Amfani Da Abinci A Matsayin Makami.
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya fadawa tokwaransa na kasar Kamaru Poul Biya kan cewa gwamnatin kasar Rasha ce ta maida abinci a matsayin makami a yakin tattalin arzikin da ta shiga da kasashen Turai wanda ya jawo tsadar rayuwa a duniya.
Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto Macron yana fadar haka a jiya Talata a lokacinda yake ziyarar aiki a birnin Yahunde na kasar Kamaru.
Shugaban ya musanta cewa takunkuman tattalin arzikin da kasashen Turai da kawayensu ne suka jawo tsadar kayaki a kasuwannin duniya.
READ MORE : Iran; Kudaden Shiga A Cikin Watanni 4 Da Suka Gabata Sun Karu Da Kashi 580%.
Kasar Kamaru dai wacce take cikin kasashe masu tasowa tana fama da tashin goron zabi na kayakin abinci da bukatun yau da kullum a kasar. Ko a cikin yan kwanakin da suka gabata an sami karancin man fetur a kasar wanda ya jawo dogayen layukan ababen hawa a biranen kasar.
READ MORE : Mutum Guda Ya Mutu Sa’ilin Zanga Zangar Nuna Kin Jinin Gwamnati A Kasar Sudan.
READ MORE : Kasar Turkiya Ta Sake Kai Wani Sabon Hari A Arewacin Kasar Iraqi.
READ MORE ; Rashin Tabukawar Kwamitin Tsaro Na Karawa Isra’ila Karfin Guiwar Ci Gaba Da Zaluntar Falasdinawa.