Shugaban Iran Ra’isa Ya Bayyana Al’ummar Ukrain A Matsayin Wadanda Suka Fada Tarkon Bakar Siyasar Amurka.
Rahotanni sun bayyana cewa shugaban sayyid Iran Ibrahim Ra’isi a ya fadi hakan ne a lokacin taron minisotoci da ya gudanar ina ya kira alummar kasar Ukrain a amtsayin wadnda suka fada tarkon bakar siyasar shaidanci ta Amurka, kana kuma ya jaddada matsayin kasar na rashin goyon bayan yaki da ake yi kuma ya bukaci a kawo karshensa don Amfanin alummar kasashen.
Yace ALummar Ukrani kamar na Afghanistan ne da Yamen da Iraki dukkan su sun fada tarkon bakar siyasar shaidanci ta Amurka ne .
Da yake ishara game da ziyarar da ministoci ko wasu jami’an gwamnati zasu kai wata kasa yace idan wani jami’I yakai ziyara wata kasar waje kuma aka rattaba hannun kan wata yarjejeniya, dole ne ta zama za ta amfani alummar Iran,
Da yake bayani game da yarjejeniyar Vieanna kuwa yace ma’aikatar harkokin wajen kasar da tawagar kasar a tattaunawar suna kokari wajentattaunawa kan muhimman batutuwa,
Yace yarjejniyar hadin guiwa ta JCPOA ba ita ce dukkan siyasar wajen iran ba, babban abin da yasa gwamnati ta samu nasara a watanni shidan farko shi ne yadda ta bibiyi dukkan al’muran ciki har da wadanda suka shafi siyasar kasashen waje da dukkan karfinta , kuma tsarin banki da na manfetur din kasar bashi da wata alaka da yarjejeniyar