Sanun a hankali hukumar kwallon kafar Afrika wato Caf tareda sabon shugaban hukumar kwallon kafar Kamaru Samuel Eto na kokarin ganin sun kamala shirye-shiryen karbar gasar cin kofin Afrika da za ta hada kungiyoyin kasashen Nahiyar 24 daga ranar 9 ga watan Janairu zuwa 6 ga watan Fabrairun shekara mai kamawa.
A cewar Patrice Motsepe Shugaban hukumar ta Caf,za a gudanar da gwaji ga mutanen da zasu halarci gasar tareda bukatar ganin kowanen su ya karbi allurar rigakafin cutar ta Korona.
A jimilce hukuma ta Caf ta bayyana cewa mutane 219 ne za ta dau nauyin su a wannan gangami karo na 33 da zai gudana kasar ta Kamaru.
Dan afrika ta Kudu Patrice Motsepe da ke shugabantar hukuma ta Caf, yayin wannan ziyara ta yau a kasar ta Kamaru zai ziyaraci filaye guda shida da za a gudanar da wasanni da suka hada da Yaounde,Olembe,Douala, Limbe, Garoua da Bafoussam.
A wani labarin na daban Hukumar kwallon kafar Ingila ta ce ‘yan kallo ba za su halarci filin wasan da za a fafata tsakanin Arsenal da Southampton a ranar Laraba ba.
A halin yanzu hukumomin na Birtaniya sun ce dukkanin kungiyoyin dake ciki da kewayen birnin London za su rika buga wasanninsu ne ba tare da ‘yan kallo ba har sai abinda hali ya yi.
Makwanni biyu da suka gabata ne dai, hukumomin Birtaniya suka sake baiwa ‘yan kallo damar shiga filayen wasa bayan tsawon lokaci ana buga wasanni ba tare da sun baiwa idanunsu abinci kai tsaye ba, domin dakile yaduwar annobar coronavirus, koda yake ba kamar yadda aka sab aba, an takaita adadin ‘yan kallon ne zuwa dubu 2, domin kiyaye dokar baiwa juna tazara.