Ita dai wannan gasa ta kunshi kungiyoyin kwallon kafa na mata daga kasashen Afirka da dama, kuma a karawar farko da akayi jiya a birnin Lagos, kungiyar Super Falcons ta Najeriya ta doke takwarar ta ta Mali da ci 2-0.
Infantino ya bayyana Najeriya a matsayin kashin bayan harkar kwallon kafa a nahiyar Afirka sakamakon irin gudumawar da take bayarwa da kuma yadda wasan ke habaka a cikin ta.
Shugaba Buhari ya godewa shugaban FIFA Infantino da yan tawagar sa, yayin da ya jaddada aniyar gwamnatin sa na ci gaba da tallafawa matasa musamman ganin yadda kwallon kafar ta zama sana’a take kuma daga darajar Najeriya a koda yaushe.
Shugaban kasar yace zai yi amfani da kwallon kafa wajen hada kan jama’ar kasa da kuma taimaka musu inganta rayuwar su, yayin da ya bayyana farin cikin sa da yadda wasan ta daga darajar wasu jama’ar kasar.
Buhari yace kungiyar kwallon kafar matan kasar ta zama abin koyi a Afirka da duniya baki daya, yayin da ‘yan wasa irin su Asisat Oshoala ta zama ‘yar Afirka ta farko da ta lashe gasar cin kofin zakarin Turai da kungiyar ta at Barcelona.
Shugaban kasar ya bukaci FIFA ta dinga sanya Najeriya a gaba wajen gudanar da harkokin ta na zuba jari da kuma taimako.
Tawagar Infantinon ta kunshi ministan wasan Najeriya Sunday Dare da shugaban hukumar kwallon kafa ta Afirka CAF Patrice Motsepe da shugaban Hukumar kwallon kafar Najeriya Amanju Pinnick.