Kasuwar hannayen jari ta kasar Chile da kudin kasar peso sun yi galaba aka dalar Amurka, bayan da Gabriel Boric ya zama zababben shugaban kasar, Gabriel mafi karancin shekaru a tarihin kasar jiya Lahadi.
Sabon zababben shugaba Gabriel Boric ya sha alwashin fadada ‘yancin bil adama da kuma inganta walwalar jama’ar kasar.
Sabon shugaba dai ya fuskanci suka sosai daga abokan hamayya, inda suke masa kallon dan gurguzu, a yakin neman zabe mai cike da rudani, Boric ya zama shugaban kasa mafi karancin shekaru a Chile da kusan kashi 56 na kuri’un da aka kada, idan aka kwatanta da kashi 44 na abokin hamayyarsa Jose Antonio Kast.
Wani abin mamaki shine abokin hamayyarsa wato Jose Antonio Kast, na masu ra’ayin rikau tuni ya taya zababben shugaba murna a shafin Twitter tun ma kafin a sanar sakamakon karshe.
A wani labarin na daban Ofishin mai gabatar da kara na kasar Chile ya bude bincike kan Shugaba Sebastian Pinera kan sayar da kamfanin hakar ma’adinai ta wani kamfani mallakar ‘ya’yansa, wanda ya bayyana a cikin tonon sililin Pandora Papers.
Shugaban dai ya yi watsi da zargin yana mai cewa tuni aka wanke shi daga duk wani laifi a binciken shekarar 2017.
Batun sayar da kamfanin ma’adinan ga ɗaya daga cikin manyan abokan Pinera ya fara ne tun a shekarar 2010, a lokacin shugabancin sa na baya.
Ana sa ran dai sabon shugaba ya kama aiki gadan gadan ba da jimawa ba.