Shugaba Paul Kagame na Rwanda a yau Juma’a ya fara ziyarar kwanaki biyu a Mozambique don karawa Dakarun kasarsa karfin guiwa a kokarin taimakawa Mozambique yakar ‘yan ta’adda da suke barna a kasar.
A watan 7 da ya gabata ne dai ta aike da Dakarunta dubu daya, Mozambique karkashin wani kokarin kasashen yankin don yakar masu jihadi da karfin tsiya da suka dade suna cin karensu ba babbaka a yankin Cabo Delgado mai arzikin skar gas dake Mozambique.
A jiya Juma’a Paul Kagame ya sauka a birnin Penba, kuma cikin abubuwanda zai yi cikin kwanakin biyu da zai yi a kasar zai gana da sojojin kasarsa da ‘yan sanda dake aikin daukin,
Dakarun kasashen waje dai sun taimakawa Mozambique farfadowa daga halin kunci da aka shiga a kasar saboda ayyukan masu jihadin.Kungiyar kasashen yankin su 16 sun yi alkawarin aikewa da gudunmawar Dakaru 1,500.
Ana ci ga da samun karuwar wadanda suka hallaka a sakamakon Iftila’in guguwa da ambaliyar da aya afkawa yankin kudancin Afrika.
A kasar Mozambique wadda iftila’in yafi shafa, yawan mutanen da suka hallaka ya karu daga 417 zuwa 446, sai kuma sama damutane dubu 600 da guguwar ta tagayyara.
A makon da ya gabata guguwar a aka yiwa lakabi da Idai ta afkawa garin Biera na Mozambique da ke gabar teku, cikin gudun kilomita 170 a Sa’a guda, daga nan kuma guguwar ta afkawa Zimbabwe da kuma Malawi inda a nan ma ta tafka barna.
A Zimbabwe mutane 259 suka hallaka a iftila’in guguwar da ambaliyar, wasu 200 suka jikkata, yayinda mutane dubu 16 suka rasa muhallansu.
A Malawi kuwa mutane 56 suka mutu, wadanda mafi akasari suka hallaka a dalilin mamakon ruwan sama babu kakkautawa, gabannin isowar guguwar, wasu 577 kuma suka jikkata, sai kuma mutane dubu 94 da suka rasa muhallansu.