“Shugaba Erdogan ya amsa tambayoyin manema labarai a lokacin da ya dawo daga Aljeriya.
“A halin yanzu ɗan’adam yana cikin halin ha’ula’i.
Waɗanda suke bin tafarkin gaskiya na tarihi su ne suke magana,” a cewar Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da yake magana a kan batun cin zalin da Isra’ila ke yi a Gaza, bayan dawowarsa daga wata ziyarar diflomasiyya da ya kai Aljeriya.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Talata da yake cikin jirgi, Shugaba Erdogan ya yi Allah wadai da mamayar da Isra’ila ke yi, yana mai alaƙanta ta da fashi da makami, tare da jaddada yadda matsayar ƙasashen duniya ke sauyawa ta ƙin goyon bayan Isra’ila.
“Lokaci ya sauya. Kuna iya ganin yadda duniya ta fara daukar mataki kan Isra’ila. Yayin da wasu gwamnatoci suka yi shiru kan mamayar da ake yi a Gaza, Alhamdu lillahi lamarin ya ankarar da mutane gane daidai da rashin adalci. Yawan wadanda ke goyon bayan Falasdinu a kan tituna na karuwa,” in ji shi.
Da yake ba da misali da gangamin da aka yi kwanan nan a Berlin da Birtaniya da Amurka da sauran ƙasashe, ya bayyana yadda ake samun ƙaruwar fafutuka har ma a cikin isra’ilan, inda mutane ke yin kira ga Firaminista Netanyahu ya sauka daga mulki.
Netanyahu na cikin wani mawuyacin hali na fuskantar shari’a. Ko ta wace hanya zai bi, ba zai tsira ba. Da fatan zai tattara kayansa ya tafi nan ba da jimawa ba,” in ji Erdogan
Ya kuma kara jaddada kiransa na hadin kan kasashen duniya don yaƙar zaluncin da ake yi a Gaza, yana mai jaddada bukatar gwamnatoci su yi daidai da dokokin kasa da kasa, da kare hakkin bil’adama da kuma kyawawan dabi’u.
Iyakar Rafah
Da ya karkata akalar zancensa kan matakai masu kyau da ake ɗauka a mashigar Rafah ta Gaza da Masar, Erdogan ya yaba da kokarin gwamnatin Masar.
Ya bayyana yadda ake samun karuwar marasa lafiyar Gaza da ke karbar magani a asibitocin birnin na Turkiyya, ya kuma bayyana aniyar ƙara saukaka kwashe majinyata.
“Muna so mu kawo dukkan marasa lafiya ba tare da ɓata lokaci ba. Ina sha’awar daukar masu bukatar aikin tiyata da sauri da wuri, musamman yara, da kuma gudanar da ayyukan jinya.”
A yayin da yake jawabi a kan killace Gaza, Erdogan ya jaddada bukatar samar da cikakkiyar dabara, wadda ta shafi dukkanin mambobin Ƙungiyar hadin kan Ƙasashen Musulmai (OIC) da Ƙungiyar Ƙasashen Larabawa.
Ya yi kira da a yi amfani da fannonin tattalin arziki da siyasa da diflomasiyya da zamantakewa da al’adu don kafa sharaɗin tsagai
ta wuta, da kai agaji ga Gaza, da kuma sake gina birnin.
Source: TRTHAUSA