Ya ce wannan yana daga cikin shirin ajandar taron da aka gudanar a cikin wannan mako, wanda ya hada shugaban kasar Masar Abdulfattah Al sisi da kuma shugaban Falastinawa Mahmud Abbas, da kuma sarkin Jordan Abdullahi na biyu a yankin Sharm Al Sheikh na kasar Masar.
Bassam ya ce, a yayin zaman, dukkanin shugabannin uku sun jadda matsayarsu taki amincewa da mamayar da Isra’ila take yi wa birnin Quds, tare da jaddada cewa wajibi ne a warware matsalar mamayar Falastinu da Isra’ila take, domin kafa kasar Falastinu mai cin gashin kanta, da babban birninta na Quds.
Sannan kuma kakakin fadar shugaban kasar ta Masar ya kara da cewa, nauyi ne day a rata a kan dukkanin kasashen duniya da su matsa lamba kan Isra’ila domin ta amince a kawo karshen wannan matsala.
A kan haka ne ma ya cea zaman shugabannin kasashen uku, an tattauna yadda za a koma tattaunawa tsakanin Falastinawa da Isra’ila, ta yadda hakan zai share hanyar komawa zuwa ga tattauna batun kafa kasar Falastinu mai cin gashin kanta.
Wasu rahotanni da kafofin yada labaran Isra’ila suka bayar sun ce, Masar da Qatar suna matsa lamba kan Hamas, kan ta dakatar da ayyukan da k tayar da hankalin yahudawa a kan iyakokin Gaza da Isra’ila, idan ta yi a nata bangaren Isra’ila za ta bude iyakokin Gaza domin shigar da abinci da sauran kayayyakin bukatar rayuwa ga al’ummar yankin.
Sai a nata bangaren Hamas ta ce duk wani batyun tattaunawa da Isra’ila ko yin aiki da sharuddan da Isra’ila ta gindaya, hakan bai shafe ta ba kuma bai shafi al’ummar Gaza ba, idan Isra’ila ta yi wani shishigi kan yankin zirin Gaza, to za ta fuskanci martani.