Shin me nene laifukan yaki kuma ko za a iya tuhumar Putin kan Ukraine.
Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya bayyana harin da aka kai a asibitin haihuwa da na yara a matsayin laifin yaƙi.
Yana iya zama kamar ba haka ba, amma “ko yaki yana da dokoki”, kamar yadda kwamitin kasa da kasa na Red Cross ya bayanna.
Wadannan suna kunshe a cikin yarjejeniyoyin da ake kira Geneva Conventions da jerin wasu dokoki da yarjejeniyoyin ƙasa da ƙasa.
Shin mene ne laifukan yaki?
Ba za a iya kai wa farar hula hari da gangan ba – haka kuma ababen more rayuwa da ke da muhimmanci ga rayuwarsu.
An hana amfani da wasu makamai saboda muguwar wahala da suke jawowa – kamar nakiyoyin da ake binnewa karkashin kasa da makamai masu guba.
Dole ne a kula da marasa lafiya da masu rauni – ciki har da sojoji da suka ji rauni, saboda haƙƙinsu a matsayin fursunonin yaƙi.
Wasu dokoki sun haramta azabtarwa da kisan kiyashi – yunƙurin kawar da wani rukunin mutane da gangan.
Manyan laifuffuka a lokacin yaki kamar kisan kai, fyade ko tsananta wa mutane , ana kiransu da “laifiukan cin zarafin bil’adama”.
Wadanne zarge-zarge na laifukan yaki aka yi a Ukraine?
Ukraine ta ce harin da jiragen yaƙin Rasha suka kai kan cibiyoyin haihuwa da na yara a Mariupol laifi ne na yaki.
An kashe mutane uku ciki har da yaro guda kuma an raunata 17 ma’aikata da marasa lafiya.
Akwai kuma rahotannin da ke cewa sojojin Rasha sun kai hari kan fararen hular Ukraine da ke tserewa.
Akwai ƙwararan shaidu da ke nuna cewa tarin bama-bamai – alburusai da ke wargajewa bayan an harba su – sun afka wa yankunan fararen hula na Kharkiv.
Rasha da Ukraine ko wanennsu bai sanya hannu kan dokar hana amfani da su ba a duk duniya, amma ana iya ɗaukar waɗannan abubuwan da suka faru a matsayin laifin yaƙi.
Ma’aikatar tsaron Burtaniya ta ce Rasha ta yi amfani da bama-baman da ake kira thermobaric, waɗanda ke haifar da wani gagarumin giɓi ta hanyar tsotse iskar oxygen.
Ba a haramta waɗannan bama-bamai masu muni ba – amma amfani da su da gangan kusa da fararen hula zai kusan karya ƙa’idojin yaƙi.
Masana da yawa suna jayayya cewa mamayewa kansa laifi ne a ƙarƙashin manufar yaƙi mai tsanani – ƙari akan wannan a ƙasa.
Ta yaya ake bin waɗanda ake zargi da aikata laifukan yaƙi?
Kowace kasa tana da alhakin gudanar da bincike kan laifukan yaƙi. Wasu al’ummomi suna yin hakan fiye da wasu.
A Burtaniya, manyan jami’an ‘yan sanda sun yi tayin taimakawa wajen tattara shaidun yiwuwar aikata laifuka a Ukraine.
Ta yaya za a gurfanar da wadanda ake zargi da aikata laifukan yaki?
Tun bayan yakin duniya na biyu ne dai ake zaman kotuna da dama – ciki har da kotun hukunta laifukan yaki da aka aikata bayan ballewar kasar Yugoslavia.
An kuma kafa wata hukuma da ta gurfanar da wasu daga cikin wadanda ke da hannu a kisan kiyashin Rwanda, inda ‘yan Hutu suka kashe mutane 800,000 a cikin kwanaki 100 a shekarar 1994.
A yau, kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) da kotun shari’a ta kasa da kasa (ICJ) suna da rawar da za su taka wajan tabbatar da ƙa’idojin yaƙi.
Kotun ƙasa da ƙasa
Kotun ta ICJ ta na shari’a kan takaddamar da ke tsakanin kasashe, amma ba za ta iya gurfanar da daidaikun mutane ba. Ukraine ta fara shari’a a can kan Rasha game da mamayar.
Idan kotun ta ICJ ta yanke hukunci a kan Rasha, aikin aiwatar da hukuncin zai koma ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya (UNSC).
Sai dai Rasha – daya daga cikin kasashe biyar masu kujerar din -din a Majalisar Dinkin Duniya – na iya yin watsi da duk wata shawara ta sanya mata takunkumi.
Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya
Kotun ta ICC tana bincike tare da gurfanar da wasu masu aikata laifukan yaki wadanda ba sa gaban kotunan kasashe.
Ita ce ta maye gurbin Nuremberg, wadda ta tuhumi manyan shugabannin Nazi da suka tsira a lokacin da suke tsare a 1945.
Nuremberg ce ta tabbatar da ka’idar cewa kasashe za su iya amincewa da kafa kotu ta musamman don kiyaye dokokin kasa da kasa.
Shin kotun ICC za ta iya gurfanar da laifuka a Ukraine?
Babban mai shigar da kara na kotun ICC, lauyan Birtaniya Karim Khan QC, ya ce akwai dalilai masu ma’ana da za a yarda cewa an aikata laifukan yaki a Ukraine – kuma yana da izinin jihohi 39 su gudanar da bincike.
Masu binciken za su duba zarge-zargen da ake yi a baya da kuma na yanzu – a koma baya har zuwa shekarar 2013, kafin Rasha ta mamaye Crimea daga Ukraine.
Idan akwai shaidu kan daidaikun mutane, mai gabatar da kara zai bukaci alkalan kotun ta ICC da su ba da sammacin kama su a gaban kuliya – wanda za a yi a Hague.
READ MORE : DRC; Mutum 75 Ne Suka Mutu Sanadiyyar Hatsarin Jirgin kasa.
A nan ne iyakoki a aikace kan ikon kotun suka bayyana.
Kotu ba ta da ‘yan sanda nata. Ta dogara ga kasashe wajan kama wadanda ake zargi.
Amma Rasha ba mamba ce a kotun – ta fice a cikin 2016. Shugaba Putin ba zai mika duk wanda ake tuhuma ba.
Idan wanda ake tuhuma ya tafi wata ƙasa, ana iya kama su – amma wannan shi ma batu ne mai tsarkakkiya
Shin za a iya tuhumi Shugaba Putin ko wasu shugabannin?
Ya fi sauƙi a ɗora laifin yaƙi a kan sojan da ya aikata shi, fiye da shugabannin da suka umarce su da su harbe su.
Amma kotun ta ICC kuma za ta iya gurfanar da laifin “yin yaki mai tsanani”.
Wannan laifi ne na mamaya ko rikici da bai dace ba.
Ya samo asali ne a Nuremberg, bayan da alkalin da Moscow ta aika ya shawo kan kawancen kasashen duniya cewa shugabannin Nazi ya kamata su fuskanci shari’a kan “laifi tada husuma”.
Sai dai Farfesa Philippe Sands QC, masani kan dokokin kasa da kasa a kwalejin jami’ar London, ya ce kotun ta ICC ba za ta iya gurfanar da shugabannin Rasha kan wannan laifi ba saboda kasar ba ta rattaba hannu kan yarjejeniyar kafa kotun ba.
A ra’ayi, kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya na iya neman kotun ICC ta binciki wannan laifi.
Amma kuma, Rasha na iya yin watsi da wannan a matsayin daya daga cikin mambobin majalisar na dindindin guda biyar.
To shin ko akwai wata hanya ta daban ta gurfanar da ɗaiɗaikun mutane?
Tasirin kotun ta ICC – da kuma yadda dokokin kasa da kasa ke aiki a aikace – ba wai kawai ya dogara bane a kan yarjejeniya ba, amma siyasa da diflomasiyya.
Kuma Farfesa Sands da sauran masana da yawa suna jayayya cewa kamar Nuremberg, mafita ta sake ta’allaka ne kan diflomasiyya da yarjejeniyar kasa da kasa.
Yana kira ga shugabannin kasashen duniya da su kafa wata kotu domin hukunta laifukan ta’addanci a Ukraine.