Sheikh Na’im Кasim mataimakin shugaban ƙungiyar Hizbullah ta ƙasar Labanon ya bayyana cewar idan da ba don martanin da ƙungiyar Hizbullah ta mayar wa Isra’ila ba, da haramtacciyar ƙasar za ta ci gaba da kawo wa ƙasar Labanon hari.
Sheikh Na’im Кasim ya bayyana hakan ne a jawabin Ashura da yayi don tunawa da shigowar watan Muharram, inda yayin da ya ke magana kan harba makamai masu linzami da Hizbullah ta yi zuwa cikin ‘Isra’ila’ a matsayin mayar da martani ga hare-haren da ta kawo Kudancin Labanon, Sheikh Кasim ya ce: Idan ba don martanin da aka yi wa Isra’ila ba, to da kuwa ta ci gaba da kawo hare-haren wuce gona da iri a kan mu”
Na’ibin shugaban na Hizbullah ya ce: Hizbullah dai ba ta son yaƙi, to amma ba za ta yi ƙasa a gwuiwa ba, kamar yadda aka gani a baya-bayan nan, wajen mayar da martani a duk lokacin da Isra’ila ta kawo harin wuce gona da iri.
Sheikh Кasim ya sake jaddada aniyar ƙungiyar na ci gaba da kare mutumcin ƙasar Labanon daga duk wani ƙoƙari na keta hurumin ƙasar, yana mai cewa Amurka dai baa bar yarda da kuma dogaro ba ne.
A ranar 5 ga watan Augustan nan ne dai Isra’ilan ta kawo hari Kudancin Labanon lamarin da ya sanya dakarun Hizbullah ɗin mayar mata da martani ta hanyar harba makamai masu linzami guda ashirin cikin yankunan da Isra’ilan ta mamaye kusa da sansanin sojanta na Douf.
Haramtacciyar kasar isra’ilan dai ta dingi kai hare hare a wasu yankuna na kasar labanan din ne wanda hakan ya tilasta kungiyar mukawama da ‘yan asalin labanan daukan matakin kare kai ta hanyar harba makamai zuwa cikiin haramtacciyar kasar isra’ilan wanda hakan ya matukar tsorata yahudawan na sahayoniya kuma suka fahumci ba za’a barsu suna kashe musulmi hakanan ba.