Shamkhany Kasashen Turai Ne Ummul Haba’isin Yake-yake A Duniya.
Shugaban majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Shamkhani ne ya bayyana hakan, sannan ya kara da cewa; Babu wani abu da ya kai yaki muni.
Ali Shamkhani ya yi ishara da yadda kasashen yammacin turai suke tsoma bakinsu a cikin harkokin kasashe,don haka su ne ke da alhakin duk wasu yake-yake da rikice-rikice da ake yi domin kalubalantar halin ketar turawa.
Tun da fari shugaban kasar Iran ya dora alhakin abinda yake faruwa a kasar Ukiraniya a wuyan kuniyar tsaro ta Nato.
Shugaban na Iran Ibrahim Raisy wanda ya yi Magana ta wayar tarho da shugaban kasar Rasha Vlademir Putin ya ce; Wanzuwar kungiyar ta Nato baraza ne ga kasashe masu ‘yanci.
Ra’isy ya kara da cewa; Ya fahimci damuwar da kasar Rasha take da shi dangane da tsaro, wanda matakan Amurka da Nato ne su ka haifar da shi.