Lauyan sa Cire Cledor ya kuma ce bayan Cesar an kuma daure wasu mutane biyu da suka hada da Omar Ampoi Bodian da dam jarida Rene Capain Bassene rai da rai a kotun dake Ziguinchor.
A cikin watan Maris na shekarar 2022,Rundunar sojin kasar Senegal ta kaddamar da farmaki kan mayakan da ke kawance da mayakan ‘yan tawayen ‘Casamance’, wata kungiyar ‘yan aware a yankin kudancin kasar.
A ranar 13 ga watan na Maris, sojojin kasar na Senegal suka kaddamar da farmakin kan mayakan ‘yan awaren na Casamance da ake kira da MFDC a takaice, wadanda suke karkashin jagorancin Salif Sadio.
Tun a shekarar 1982 mayakan ‘yan awaren na Senegal suka fara fafutukar yaki da gwamnatin Senegal, bisa zargin gwamnatin kasar da mayar da su saniyar ware.
Mutane 16 ne aka tuhuma da laifin kashe mutane 14 da suka je daji omin neman itace a Bayotte dake kusa da Ziguinchor ranar 6 g awatan Janairun shekarar 2018.
A wani labarin na daban kasar Senegal ta bayyana takaicin ta dangane da kalaman da ‘dan takaran shugaban kasar Faransa mai ra’ayin rikau Eric Zemmour yake yi dangane da nuna wariyar jinsi a kan jama’ar kasar ta da kuma bukatar ganin an kore su a Faransa.
Yayin wata hira a talabijin, Zemmour ya bayyana cewar duk masu safarar mutane a Faransa sun fito ne daga kasar Senegal, saboda haka ya dace a kore su da zaran ya zama shugaban kasa.
Jakadan Senegal a Faransa El Hadji Magatte Seye ya bayyana kalaman a matsayin nuna wariyar jinsi da cin zarafin jama’ar kasar sa wanda zai shafi dangantakar kasashen biyu.
Seye ya ce wadannan kalamai na Zemmour wani cin zarafin mutanen Senegal ne da ba zas u amince da shi ba lura da yadda jama’ar kasar ke mutunta dokokin Faransa.
Jakadan ya ce za su dauki matakin diflomasiya wajen ganin ‘dan takarar ya janye wadannan kalamai.