Sayyid Ra’isi Ya Jaddada Aniyar Iran Ta Habaka Harkar Ilimin Kasarta.
Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Al’ummar Iran ba za ta taba dakatar da ayyukan da take gudanarwa domin ci gaban kasarta ba.
A jawabinsa a wajen bikin girmama malaman jami’a da dalibai da suka samu nasarori a bangarorion daban-daban na ilimi, shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi ya jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta la’akari da farin ciki ko bakin cikin wasu mutane kan hubbasar da take yi a fagen bunkasa harkokin ilimi da ayyukan ci gaban kasarta, iyaka dai tana la’akari ne da hakkinta na samar da ci gaba a dukkanin bangarorin rayuwa, don haka babu abin da zai dakatar da ita ko kokarin mai da ita baya.
READ MORE : Shugaban Kasar Mauritaniya Ya Isa Saudiyya Domin Gudanar Da Aikin Hajji.
Haka nan Sayyid Ra’isi ya yaba wa masana da manazartar kasar Iran kan kokarin da suke yi na bunkasa ci gaban kasarsu musamman fadada fannonin ilimi da bincike sannan gudanar da ayyukan ci gaban kasa a dukkanin bangarorin rayuwar al’umma.
READ MORE : Iran Da Venezuela Sun Jaddada Wajabcin Kara Karfafa Kawance Da Alakoki A Tsakaninsu.
READ MORE : Tsohon Shugaban Burkina Blaise Compaoré Zai Koma Gida.