Sayyid Nasarallah; Babu Dangantaka Tsakanin Tattaunawar JCPOA Da Shata Iyakar Ruwa Da Isra’ila.
Sakatare Janar na kungiyar Hizbullah ta Kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasarallah ya bayyana cewa babu wata dangantaka tsakanin tattaunawar farfado da yarjejeniyar JCPOA ta shirin Nukliyar kasar Iran da ke gudana a halin yanzu a birnin Vieannan da kuma batun shata kan iyakar ruwa a yankin Karish tsakanin gwmanatin kasar Lebanon da Isra’ila (HKI).
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shugaban kungiyar yana fadar haka a jiya, a bikin bude cibiyar yawon bude ido na kungiyar a yankin Bikaa kuma garin Janta, inda nan ne kungiyar ta fara kafa sansaninta na farko shekru kimani 40 da suka gabata.
Sayyid Nasarallah ya kara da cewa idan an cimma yarjejeniya kan iyakar ruwa tsakanin HKI da Lebanon za’a zauna lafiya idan ba hakaba akwai tashin hankali nan gaba.
Da ya sake komawa kan cibiyar ajiya kayakin tarihi na kungiyar a Janta kuma Nasarralah y ace garin ya cancanci hakan, don daga nan ne kungiyar ta fadada sauran sansanoninta zuwa dukkan yankin kudancin kasar Lebanin a yake yaken da ta shiga da HKI shekaru 40 da suka gabata. Kuma mutanen garin Janta sun cancanci yabo don tare da taimakonsu yan kadan aka fara wannan gwagwarmayar wacce ta sami nasarori masu yawa daga baya.