Sayyid Hassan Nasrullah Ya ce Rusa Masallacin Quds Yana Nufin Rushewar Isra’ila.
A cikin jawabin da yayi na ranar Quds ta duniya a jiya juma’a sakatare janar din kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon sayyid Hassan nasrullah ya gargadin gwamnatin sahyuniya game da duk wani ganganci kan Masallacin Kudus ya ce rusa masallacin Quds dai dai yake da rushewar Isra’ila daga doron kasa.
Yace yan gwagwarmaya na ci gaba da yin arangama da Isra’ila tare da samun nasarori duk kuwa da matsin lamba da takurwar da take yi da ma magoya bayanta,
Kana ya bukaci kasashe da sauran sojoji dake yankin da su isar da wannan sako ga Isra’ila cewa duk wani gangaci na rusa masallacin kudus, to yana nufin rusa Isra’ila ken an baki daya, kuma ta sani cewa duk wani yunkurin keta hurumin masallacin Quds zai iya haifar da yaki a yankin tsakaninta day an gwagwarmaya
Da yake ishara game da barazanar da Isra’ika ta yi kan Atisayin da za’a yi a nan gaba sayyid nasrullah ya fadi cewa yan gwagwarmaya sun gudanar da Atisayin soji a makwanni biyu da suka gabata kuma sun gargadi isra’ila game da duk wani gigin na kai mata hari ta sani cewa ba zai wuce hakan nan ba ba tare da mayar da martani ba.