Sayyid Hassan Nasrollah Ya ce Amincewa Da Amurka Wauta Ce Babba .
Babban magatakardar kungiyar hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hassan Nasrollah da yabe jawabi a ranar bukin tunawa da ranar soji da aka jikkata na kungiyar ya fadi cewa amincewa da Amurka wauta ce sosai.
Da yake tsokaci game da takin da ake tafkawa tsakanin Rasha da Ukrain ya fadi cewa Amerika tace tana duba irin take hakkin bil adama da kasar rasha ta yi a Ukranin , amma me za ta ce game da takin hakkin dan Adama a yamen da heroshima da Nakazaki, kasar Amurka ta kai harin masu bikin Aure a Afghanistan ta mayar da shi ya kuma zaman makoki.
READ MORE : Dakarun Kare Juyin Musulunci Na Iran Sun Yi Alwashin Daukar Fansa Kan Isra’ila.
Haka zalika yace me zai ci game da irin cin zarafin bil adama da Isra’ila take yi, me yasa har yanzu ba’a ji tayi tir da harin ta’addanci da aka kai a a wani masallaci a Pakistan a ranar jumaa da ta gabata ba. Inda mutane da dama suka mutu ciki har da limamin masallacin saboda yan ta’addan da suka kai harin Amurka ta kirkiro su.
Daga karshe sayyid Nasrullah ya nuna cewa amincewa da Amurka wauta ce babba, yace shugaban kasar Afghanistan dake gudun hijira yanzu haka, ya kasance na hannun daman Amurka ya fadi cewa babban kuskuren da ya yi shi ne ya amince da Amurka kuma ya dogara da ita