Ƙungiyar agaji ta Save the Children ta yi gargaɗi kan cewa idan ba a ɗauki ƙwakkwaran mataki ba, kusan yara 230,000 da masu jego a Sudan za su iya mutuwa saboda yunwa.
Tayar da bama-bamai da lalata wurare da kamfanoni ya sa Sudan ta koma cikin ɗaya daga cikin ƙasashe “mafi muni” ta ɓangaren ƙarancin abinci a duniya, kamar yadda Arif Noor ya bayyana, wanda shi ne daraktan Save the Children a Sudan.
“Kusan yara 230,000 da mata masu ciki da masu jego za su iya mutuwa a cikin watanni masu zuwa,” kamar yadda ƙungiyar ta bayyana.
Ƙungiyar ta ce “sama da yara miliyan 2.9 da ke Sudan na fama da ƙarancin abinci da matsakaiciyar yunwa inda wasu 729,000 din ke cikin matsananciyar yunwa.”
Yaƙin wanda masana suka yi gargaɗi kan cewa zai iya ɗaukar shekaru ana gwabzawa ana yin sa ne tsakanin Shugaban Sojin Sudan Abdel Fattah al-Burhan da Mohamed Hamdan Daglo wanda shi ne shugaban Rundunar RSF.
Yanayin yunwa
Noor ya yi gargaɗi kan cewa halin da ake ciki zai ƙara taɓarɓarewa idan aka ci gaba da wannan rikicin.
“Rashin shuka a bara na nufin babu abinci a yau. Rashin shuka a yau na nufin babu abinci a gobe. Yanayin yunwar zai ci gaba da ƙaruwa ne ba tare da ganin ƙarshenta ba,” in ji shi.
Sakamakon rikicin da aka shafe watanni 11 ana yi tsakanin janarori biyu a Sudan ɗin, dubban mutane sun rasa ransu mutum miliyan takwas kuma sun rasa muhallansu, kamar yadda Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana.
Majalisar Dinkin Duniya ta kara da cewa, fiye da rabin dukkan ‘yan kasar Sudan, ciki har da yara miliyan 14, na bukatar agajin jin kai don tsira.
Wani rahoto da Hukumar Kare Hakkin Bil’adama ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta fitar ya nuna yadda aka gudanar da cin zarafi iri daban-daban waɗanda suka saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa.
DUBA NAN: Yunwa ta kashe wasu yaran Falasdinawa biyu
Wannan rikicin ya sa mutum miliyan 18 cikin halin rashin abinci daga ciki har da mutum miliyan biyar da suka kusan shiga cikin yunwa.