Bankin Duniya ya yi gargadin cewa, karancin albarkatun gona da rashin ruwa da kuma tumbatsar tekuna da sauran matsalolin sauyin yanayi, ka iya tilasta wa mutane miliyan 216 kaurace wa muhallansu nan da shekarar ta 2050.
A wancan rahoto, bankin ya yi hasashen cewa, mutane miliyan 143 za su iya kaurace wa muhallansu a wadannan yankuna na duniya nan da shekarar ta 2050.
A sabon rahoton da ya fitar kuwa da ya kunshi sabbin yankuna uku da suka ha da da Gabashin Turai da Tsakiyar Asiya da Arewacin Afrika da kuma Gabashin Asiya har ma da yankin Pacific, bankin ya rubanya adadadin yawan mutanen da wannan matsala za ta shafe su nan da 2050.
Koda yake mataimakin shugaban bankin na duniyar bangaren samar da ci gaba, Juergen Voegele, ya ce, wannan adadi da suka yi hasashe ka iya sauyawa .
A cewarsa, muddin kasashen duniya suka fara rage gurbata muhalli da kuma maido da kyakkyawar alaka tsakanin halittu da muhalli, sannan kuma mutane suka sauya halayensu, to babu shakka za a samu raguwar kaurace wa muhalli da kashi 80 cikin 100 nan da shekarar ta 2050.
Ma’ana dai, adadin zai koma miliyan 44 a maimakon miliyan 216 da aka yi hasashen za su yi kaurar ta tilas saboda tasirin sauyin yanayi.