Ministan harkokin wajen amurka Amir-Abdullahiyan ya bayyana cewa sauran batutuwa da suka rage a tattaunawar da akeyi a birnin domin vienna domin farfado da yarjejeniyar nukilyar Iran da sauran kasashen yammacin turai tana bukatar cikakkiyar kulawar amurka gami da daukar matakin daya doya kamata domin cimma matsaya wacce zata bada damar farfado da yarjejeniyar.
A wata tattaunawar wayar tarho tsakanin sa da takwaran sa na belgium Sophie Wilmes, ministan harkokin wajen na Iran ya bayyana shirin kasar sa na kyautata alakar ta kasar ta belgium a bangarorin tattalin arziki da sauran su.
Da yake bayyana alakar dake tsakanin kasashen biyu Abdollahiyan ya tabbatar da cewa alakar Jamhuriyar musulunci ta Iran da Belgium an gina ta ne bisa kyautatawa da kuma mutunta juna tsawon shekarun da suka gabata.
A bangaren tattaunawar vienna wanda ake gudanarwa tsakanin Jamhuriyar musulunci ta Iran da kasashen yammacin turai minsitan harkokin wajen na Iran ya tabbatar da cewa zuwa yanzu an cimma wani mataki mai muhimmanci na farfado da yarjejeniyar ama abinda ya rage kawai shine kasar amurka ta dauki matakin daya dace domin a cimma gaci a wanna tattaunawa.
Abdollahiyan ya tabbatar da cewa kuma wakilin majalisar tarayyar turai ne yake kula da lamarin kamar yadda kafar yada labaran su ta tabbatar.
A nasa bangaren minsitan harkokin wajen belgium ya bayyana wasu daga cikin yarjejeniyar da Iran din da belgium suka shiga gami da ayyukan da suka hada kasashen biyu a tsawon shekaru.
Wilmes ya bayyana abubuwan da suka hada kasashen biyu kama daga bangarorin tattalin arziki da sauran su.
Iran da sauran kasashen yammacin turai dai sna gudanar da tattaunawa domin farfado da yarjejeniyar tattalin arziki ta (JCPOA) ne dai a birinin vienna tun watan afrilun daya gabata.
Hakan ya biyo bayan ficewar da tsohon shugaban amurka donald trump yayi daga yarjejeniyar a shekara 2018.