Rahotanni sun tabbatar da cewa kasar saudiyya ta tuntubi gwamnatin haramtacciyar kasar isra’ila domin sayan makamai masu linzami daga wajen isra’ilan a dai dai lokacin da fadan saudiyyan da musulmin kasar yemen ya dau zafi.
Jaridar ”Breakin Depence Magazine” ce ta wallafa labarin inda ta tabbatar da cewa ta samu labarin daga wasu majiyoyi da suka fito daga kasar isra’ila.
Wannan mataki dai yana zuwa ne a dai dai lokacin da kasar amurka ta cire manyan na’urorin tsaron kare kai din ta daga babban riyadh babban birnin kasar da saudiyya.
Bayan cire na’urorin a ranar lahadi, ”pentagon” a ta bakin mai magana da yawun john kirbi ta tabbatar da cewa zata cigaba da cikakkiyar alaka da abokan ta na nahiyar gabas ta tsakiya duk da cire na’urorin tsaron na maurka daga babban birnin saudiyyan.
Rahotanni sun tabbatar da cewa masarautar saudiyya tana duba yiwuwar tuntubar kasar chana da rasha a matsayin wadanda zasu samar mata da wadannan na’urori.
Ana ganin dai saudiyyan na iya sayan makami mai linzamin nan na ”Irone Dome” ko kuma ER Barak duk mallakin haramtacciyar kasar isra’ilan a matsayin makwafin makaman kare kai da amurkan ta cire daga babban birnin riyadh din.
Masana harkokin yaki sun tabbatar da cewa ko da saudiyya ta iya mallakar makaman kariyar daga haramtacciyar isra’ila ba zata iya kare kanta daga hare haren ramuwa da yemen zata iya kawo mana ba , kuma masanan sun buga misali da yadda ita kanta haramtacciyar kasar isra’ilan ta kasa kare kanta daga haren haren ramuwar da falasdinwa suka kai mata a watan mayun daya gabata.
Rahotanni sun tabbatar da cewa mahukuntan masarautar saudiiyan dai suna cikin tsaka mai wuya domin kowanne lokaci yemen na iya kai musu harin ramuwa bisa kashe kashen fararen hula saudiyyan taek da aiwatarwa a kwanakin nan.
A baya dai kasar jamhuriyar musulunci ta Iran ta taba bugar kirjin bama saudiyyan kariya idan tana so kuma a kyuata ba kuma tare da wulakanci irin yadda amurka da saurn kasashe kema saudiyyan ba amma saudiyyan bata amshi wannan tayi ba duk da nuna alamun amsawa da tayi da fari.