Saudiyya ta yi tir da masu kona AlKur’ani.
Gwamnatin Saudiyya ta yi tir da masu tsattsauran ra’ayi na kasar Sweden da suka kona Alkur’ani mai tsarki da “gangan” tana mai cewa sun yi hakan ne domin su takali fada da kuma hasala Musulmai.
A wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, Ma’aikatar Harkokin Wajen kasar, ta bayyana muhimmancin tattaunawa da amincewa da juna da kuma zaman tare.
Sanarwar ta kuma jaddada bukatar kyamar tsattsauran ra’ayi da kiyayya. Saudiyya ta kuma bayyana bukatar kawar da dukkan arangama tsakanin mabiya mabambantan addinai a wurare masu tsarki.
READ MORE : Iraqi Ta Kira Jakadanta A Sweden Bayan Kona Al Kur’ani A Kasar.
Mutane uku sun jikkata babban birnin Norrkoping na kasar Sweden bayan ‘yan sanda sun harba musu alburusai lokacin wata taho-mu-gama tsakaninsu bayan kona Alkur’ani, lamarin da ya haifar da zanga-zanga a garuruwa da dama na kasar a karshen mako lokacin bikin Easter.
READ MORE : Rasha Ta Yi Gargadi Akan Yiyuwar Batakashi Da Kungiyar Tsaro Ta “ Nato” A Yankin “ Artic’.