Kamar yadda press t.v ta rawaito, sojojin kasar yemen sun tabbatar da cewa a wata fafatawa da akayi sojan sa kai karkashin jagorancin saudiyya sun kwashi kashin su a hannu wanda hakan ya tilsata mus ja da baya a yakin da ake gudanarwa.
A firar kai tsaye da tashar ta press t.v tayi da dan arajin kare hakkin dan adam dinna, hussain albukaiti ya tabbatar da cewa yanzu sojojin yemen sun kusa kwace gabadayan yankin ma’arib daga hannun sojin sa kan na saudiyya, wand ada yankin na ma’arin yana hannun sojin sa kan saudiiya din.
Sai dai an jiyo kafafen yada labaran saudiyyan suna ikirarin sun kashe sonin yemen 92.
Da aka tuntubi daya daga cikin manyan jami’an gwamnatin yemen ya tabbatar da cewa, saudiyyan matsorata ne basa iya gaba da gaba da sojojin yemen, kuma wadanda suka kashe fararen hula ne mutanen gari kamar yadda aka sani saudiyyan ta kai harin boma bomai ne a wani shagon sayar da magunguna.
Idan da gaske yaki sukeyi kuma ba matsorata bane me yasa zasu kai hari shagon sayar da magunguna? me ya hada sojoji da shagon sayar da magunguna? sojoji suna fagen daga ana fafatawa, a ta bakin wani babban jami’in gwamantin Yemen.
Bincike dai ya tabbatar da cerwa saudiyya tana tafka asarori a kallafaffen yakin data kallafawa kanta da al’ummar yemen din kuma babban abin banhaushin shine bata iya tunkarar sojin yemen din sai dai hare hare da take ta faman kaiwa a kan fararen hula wadanda basu ji ba basu gani ba.
Tuni dai al’ummomin duniya da dama sukayi tirr da halin saudiyyan na kai hari kan raunana a yemen din kuma masu rajin kare hakkin dan adam na duniya sukayi kira ga kasashen duniya dasu kawo karshen wanna ta’addanci da saudiyya din domin samun zaman lafiya ayankin gabas ta tsakiya dama duniya baki daya