Saudiyya Ta Sallami Fursunonin Yemen,163.
Kawancen da Saudiyya ke jagoranta kan yaki a Yemen, ya sanar da sakin fursunoni 163 a wani mataki na karfafawa shirin zaman lafiya da tattaunawa na tsakanin ‘yan Yemen.
Sanarwar da kawancen ya fitar ta ce jirgin saman farko ya kwashe rukunin farko na fursunoni 108 zuwa Aden, sai kuma guda 9 zuwa Sanaa.
Baya ga hakan akwai wasu ‘yan kasashe ketara guda tara da ba’a bayyana asalinsu ba da sanarwar ta ce an mika su ga ofisoshin jakadancin kasashensu.
Kungiyar agaji ta (CICR), ce ke taimakawa wajen jigilar fursunonin daga Saudiyya zuwa Yemen.
READ MORE : Hungary Ta Takawa (EU) Birki Kan Kakabawa Man Fetur Din Rasha Takunkumi.
Kakakin tawagar kungiyar, a Yemen, Bachir Omar, ya shaidawa Arab News cewa, ko wane fursuna ana maida shi yankinsu ne na asali ko kuma gwagwadon zabinsa, saboda dalilai na tsaro.
READ MORE : Abdollahian Da Guteress, Sun Zanta Kan Batutuwa Da Dama Da Suka Shafi Kasa Da Kasa.
READ MORE : Kungiyoyin Gwagwarmayar Falastinawa Sun Dora Alhakin Abin Da Ke Faruwa A Kan Gwamnatin Isra’ila.
READ MORE : Khatibzadeh; Yin Tsayin Daka A Gaban ‘Yan Mamaya A Quds Da Falastinu Hakki Ne Halastacce.