Saudiyya Ta Lamunce Mutum Miliyan Daya Su Yi Aikin Hajji A Bana.
Saudiyya, ta sanar da cewa za ta baiwa mutum miliyan daya, damar yin aikin hajji a bana, shekaru biyu da takaita adadin sakamakon bullar annobar korona.
Wata sanarwar da ma’aikatar kula da aikin hajji da Umara ta Saudiyya ta fitar ta ce za’a kara adadin wadanda zasu zo aikin hajjin daga ketare zuwa miliyan daya.
Masu niyyar zuwa aikin hajjin na bana zasu kasance masu shekara kasa da 65, sannan ya kasance sun yi cikakkun alluran riga kafin cutar korona a cewar sanarwar da kamfanin dilancin labaren kasar na SPA ya rawaito.
Haka zalika maniyatan zasu nuna takardar gwajin dake nuna cewa basa dauke da cutar ta korona, sannan kuma za’a gudanar da aikin hajjin cikin kiyaye matakan yaki da cutar.
READ MORE : Will Smith Ya Karbi Hukuncin Harmacin Halartar Wasan Oscar Na Shekaru Goma.
A bara dai ‘yan Saudiyya 60,000, mahukunatan kasar suka baiwa damar yin aikin hajjin, maimakon miliyan 2 da rabi da suka saba sauke farali kafin bullar annobar korona.
READ MORE : EU Ta Laftawa ‘Ya’Yan Putin Da Wasu ‘Yan Rasha Fiye Da 200 Takunkumi.
READ MORE : Buhari Ya Nemi A Kara Kudaden Tallafin Mai Zuwa Naira Tiriliyan 4.