Saudiyya ta ƙara yawan waɗanda za su Hajjin bana zuwa miliyan ɗaya.
Saudiyya ta ƙara adadin maniyyatan bana zuwa miliyan ɗaya daga ciki da wajen kasar, kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar SPA ya ruwaito.
Ma’aikatar kula ayyukan Hajji da Umrah ta kasar Saudiyya ce ta sanar da matakin ƙara yawan masu aikin Hajjin hajjin zuwa miliyan daya daga ciki da wajen Saudiyya.
Adadin ya ƙaru idan aka kwatanta da shekaru biyu da suka gabata, saboda annobar korona wanda ya tilasta wa Saudiyya rage yawan waɗanda za su aikin Hajji.
READ MORE : Azhar Watch Ta Yi Gargadi Kan Ci Gaba Da Cin Zarafin Mata Musulmi A India.
Sanarwar da hukumomin Saudiyya suka fitar sun ce an hana wa waɗanda suka haura shekara 65 zuwa aikin Hajjin bana.
READ MORE : Dubban Falastinawa Sun Yi Sallar Juma’a Farko A Watan Ramadan A Masallacin Quds.
Ƴan ƙasa da shekara 65 da za a bari su yi aikin Hajjin sai sun yi allurar rigakafin korona da ma’aikatar lafiya ta Saudiyya ta amince da ita.
READ MORE : Iran Da Kuwait Sun Tattaunawa Kan Batutuwa Da Suka Shafi Gabas Ta Tsakiya.
READ MORE : Rasha Ta Kori Amnesty Da Human Rights Watch.
READ MORE : Mutane 50 Sun Mutu A Harin Da Aka Kaiwa Tashar Jiragen Ukraine.