Saudiyya da Masar sun bukaci a dakata da luguden wuta tsakanin Isra’ila da Falasdin.
Kasashen biyu sun bayyana rashin jin dadinsu ga yadda lamarin ke kara ta’azzara a yanzu.
Saudiyya ta bukaci jami’an diflomasiyya da su tinkari Isra’ila kan kisan gilla ga Falasdinawa Ministocin harkokin wajen Masar da Saudiyya na kira da a tsagaita wuta nan take a fadan da a ke tsakanin Isra’ila da Hamas a Zirin Gaza, Al Arabiya ta ruwaito.
Hakan ya fito ne a cikin wata sanarwa a ranar Asabar wacce kamfanin dillacin labarai na Saudiyya ya fitar. Sanarwar ta ce Ministan Harkokin Wajen Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan ya yi magana da Ministan Harkokin Wajen Masar Sameh Shoukry.
Ta kuma bayyana, dukkansu sun amince cewa ana bukatar tsagaita wuta nan take.
Misira na ta kokarin sasantawa don dakatar da zaluncin israila kan falasdinawan.
Sanarwar ta Saudiyya ta kuma ce jami’an diflomasiyyar biyu sun yi kira ga “gamayyar kasa da kasa da su tinkari munanan ayyukan da Isra’ila ke yi wa al’ummar Falasdinawa ‘yan uwansu.”
Amma ana ganin wannan goyon bayan da saudiyya ta nuna ma falasdinawa a matsayin babarodo domin ba’a jima ba kasar saudiyya din da sauran kasashen larabawa suka daidaita da haramtacciyar kasar ta isra’ila wanda ake ganin hakan ne ya bama yahudawan sahayoniyan karfin gwuiwar sabunta sabon salon zalunci a kan al’ummar falasdinawan.
A wani labarin, Isra’ila ta ci gaba da kai hare-hare kan sassa daban daban na zirin gaza, ciki har da makamin rokar da ta harba kan gidan babban jagoran kungiyar Hamas Yehya Al Sinwar, BBC ta rahoto.
Babu tabbaci kan adadin mutanen da aka kashe ko suka ji raunuka a hare-haren da aka shafe kwana bakwai Isra’ila da Hamas na kai wa juna hari. Kungiyar Hamas ta mayar da martani ta hanyar harba rokoki da dama zuwa wasu biranen Isra’ila a wani mataki na ramuwar gayya bayan kai musu hari da Isra’ila ta yi.