Satar dan siyasar America daga dan Nigeria.
Wani ɗan majalisar wakilan Amurka ɗan jam’iyar Republican ya sanar da ajiye muƙaminsa bayan samunsa da laifin zabga ƙarya kan batunwani tallafin kudi na siyasa da ke da alaka da wani attajiri dan Najeriya.
Jeff Fortenberry ya wakilci Jihar Nebraska tsawon shekara 17.
A ranar Alhamis, masu taimaka wa alkali yanke hukunci, na tarayya suka gano cewa Jeff Fortenberry ya yi wa jami’an hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka, FBI, karya kan karbar dala dubu talatin daga wani babban atajiri ɗan Najeriya.
READ MORE : Amurka ta yi amai ta lashe a kan shugaban Rasha.
Mista Fortenberry ya ce zai sauka a ƙarshen wannan watan da muke ciki.
Haka kuma akwai yiwuwar zai shafe shekara 15 a gidan yari kuma idan haka ta tabbata a watan Yuli mai zuwa za a tasa ƙeyarsa zuwa can.
READ MORE : Farashin Danyen Mai Ya Kai Dala 120 Bayan Harin Da Akai A Matatar Aramco.