Sarkin sarakunan gargajiyar yankin Abomey, a kudancin kasar jamhuriyar Benin, Dadah Kêfa Sagbajou Glèlè ya mutu a makon da ya gabata, kamar yadda wani kusa daga masarautar yar karamar kasar yankin yammacin Afrika ya sanar da kamfanin dillancin labaran AFP a yau.
Kamar dai yadda ala’adun yankin su ka tanada haramun ne a yayata mutuwar sarki saboda mutunta halayen sa na sirri, sai dai a yi amfani da salon magana wajen sanar da cewa sarki ya mutu, misali kamar a ce dare ya fada kan Abomey”, babban birnin masarautar, da wani lokaci aka fi sani da masarautar Dahomey tsohon sunan jamhuriyar Benin.
An dai nada marigayin kan karagar ne a watan janairun 2019, dan shekaru 90 a duniya, Dadah Sagbadjou Glèlè, tsohon limamin kirsta ne da ya gaji tsohon sarki Dadah Dédjalagni Agoli-Agbo, da ya mutu a watan yulin 2018 bayan ya share tsawon shekaru 30 kan karaga.
Mutuwar sarki Sagbadjou Glèlè ta abku ne wata guda bayan bayyanarsa ta karshe a bainar jama’a albarkacin shagulgulan sake mayarwa jamhuriyar Benin kayan tarihinta da faransa ta yi a birnin Cotonou, kayayakinn tarihi 26 ne mallakar masarautar ta ‘Abomey da turawan mulkin mallakar Faransa suka yi awon gaba da su a karni na 19 ne aka mayar
Inda a wancan lokacin marigayin ya sanar da kamfanin dillancin labaran AFP matukar farincikinsa da ganin faruwar hakan ya na raye.