Babban kwamandan rundunar kare juyin juya halin musulunci na Jamhuriyar Musulunci ta Iran Sardar Salami ya bayyana yadda makiya suka tsorata duba da yadda suke ta aiko da sakonni ta hanyoyi daban daban suna rokon nizamin musulunci na Iran da kada ya dauki matakin soji a kan su.
Manjo Janaral Salami ya bayyana hakan ne a waje taron karrama Hassan Tehrani, wanda aka yima laqabi da ”Baban makaman mizayil na Iran” karo na goma saha daya.
”Yanzu muna lissafin kwanaki ne da makiya suka rasa samun nutsuwa, kuma suke ta aiko mana da sakonnin magiya” Manjo salami ya kuma bayyana cewa kasashe da dama ne suka aiko da sakonnin su ta hanyoyi mabambanta.
Manjo Sardar Salami ya bayyana cewa, makiya sun so su sanya mu cikin rikicin cikin gida domin hana mu kaiwa ga manyan hadafofin mu.
A bisa hakan kasashen turai sukayi amfani da mutuwar Mahsa Amini domin cimma mugayen hadafofin su.
” A wannan yanayin ne kuma muka fafattataki ‘yan adawa da Iran dake yankin kurdistan na Iraqi, mun kusa gwada babbar roket mai dauke da satelite mai suna ”Bavar 373 settelite” mai cin nisan zango kilomita 300, kuma jiya muka sanar mun samar da sabon makamin mizayil wanda babu tsarin tsaron wata kasa da ya isa ya tsayar da shi idan aka harba shi”
Da ya juyo bangaren yadda Iraniyawa suka fito muzaharorin kin jinin Amurka a satin da ya gabata ya bayyana cewa, Iraniyawa sun nuna a fili basa tare da munafukai.
Ma’aikatar leqen asirin Iran dai a ranar 28 oktoba ta sanar cewa ‘yan rigingimun da aka samu a Iran dina watan daya gabata dasisar kasashen yammacin turai da kafafen yada labaran s ne, wadanda suka dinga yada labaran karya dangane da dalilin mutuwar Mahsaa Amini tun kafin binciken wadanda abin ya shafa ya bayyana.
Wanda daga baya gaskiya ta bayyana kuma kowa ya gane makircin da aka kulla.