Yau Sarauniyar Ingila Elizabeth ta biyu ta cika shekaru 98 a duniya, inda rundunar sojin Birtaniya ta gudanar da bikin karrama ta, ta hanyar fareti da kuma harba bindigogi kamar yadda aka saba gudanarwa.
Sashen makadan sojin da ake kira ‘Coldstream Guards‘ sanye da jajayen kaya da huluna na kawa, sun buga taken karrama Sarauniyar a fadar ta dake Windsor a Yammacin Birnin London. Rahotanni sun ce an ci gaba da harba bindigogi a sassa daban daban na kasar Birtaniya ciki harda tsaunin Landan da akafi sani da Turanci a matsayin ‘London Tower’.
Sai dai Sarauniyar, wadda itace shugabar kasa mafi yawan shekaru a duniya, ta gudanar da bikin cika shekaru 96 ba tare da wasu hidimomin da aka saba ba, inda ta koma yankin Sandringham domin gajeruwar hutu.
Saboda yawan shekaru, Sarauniya Elizabeth ta taikata bayyanar ta a idan jama’a, inda dan ta Yarima Charles ya karbi ragamar tafiyar da wasu ayyukan da ta saba gudanarwa.
Shugabannin kasashen duniya na ci gaba da aike mata da sakon taya murna.
A wani labarin na daban ministan cikin gidan Faransa Gerald Darmanin ya nemi gafara akan yadda ‘yan sandan kasar suka yi amfani da hayaki mai sa hawayen da ya wuce kima lokacin wasan karshe na cin kofin zakarun nahiyar Turai tsakanin kungiyar Real Madrid da Liverpool a karshen mako.
Yayin da ya gurfana a gaban Majalisar Dattawa domin amsa tambayoyi akan korafe korafen da suka biyo bayan wasan karshe na cin kofin zakarun nahiyar Turan, ministan ya ce amfani da hayaki mai sa hawayen ya hana samun tirmitsitsi wajen shiga filin wasan, sai dai ya ce abin takaici hayakin ya yiwa kananan yara illa.
Saboda haka ministan wanda ya bayyana cewar akalla mutane sama da 110, 000 suka ziyarci filin wasan karshen, ya nemi gafara game da amfani da hayakin mai sa hawaye, yayin da ya ce za a hukunta jami’an ‘yan Sandan da suka harba hayakin.
Shugaba Emmanuel Macron ya bukaci gudanar da bincike na hakika dangane da lamarin, lura da yadda ministan cikin gidan ke ci gaba da fuskantar tuhuma dangane da rawar da ‘yan Sanda suka taka.
Ministan ya ce akalla magoya bayan Liverpool 30,000 zuwa 40,000 suka je filin ba tare da tikitin shiga wasan ba.