Tashar ITV ta bayar da rahoton cewa, kwamitin kwararru na masarautar Burtaniya kan ayyukan fasaha na musamman a kasar, ya sanya babban masallacin Cambriege a cikin jerin muhimman wurare da aka yi amfani da fasaha ta musamman wajen gina su a kasar.
Rahoton ya ce, a halin yanzu an sanya wannan masallaci cikin lissafi kuma yana cikin wurare guda 54 aka sanya matsayin muhimman wurare da aka yi amfani da fasaha ta musamman wajen gina su a shekara ta 2021.
A wani labarin na daban kwamitin yana bayar da kyautuka na musamman a kowace ga cibiyoyin da aka zaba domin karfafa ayyukan bunkasa al’adu da kuma fasaha a kasar.
Bangaren yada labarai na hubbaren Imam Hussain (AS) ya sanar da cewa, an fara shirin tarbar baki masu shirin gudanar da ziyarar arba’in na Imam Hussain (AS) a wannan shekara.
Shugaban kwamitin kula da shirya taruka a hubbaren Imam Hussain (AS) Sayyid Sadeq Samir Alyasiri ya bayyana cewa, an fara shirin tarbar masu ziyara kamar yadda aka saba yi a kowace shekara.
Ya ce kamar shekarar bara, a shekarar bana ma dukkanin shirye-shiryen suna kasancewa ne bisa tsauraran matakai na kiwon lafiya, sakamakon yaduwar cutar corona.
Baya ga haka kuma ya bayyana cewa, an yi tsare-tsare a bangaren yadda tarukan za su kasance da kuma da kuma wuraren hutuwa ga matafiya da suke shigowa Karbala daga bangarori daban-daban na birnin.
Ya ci gaba da cewa, dangane da matakan tsaro kuwa, tun daga lokacin tarukan Ashura da aka gudanar sama da wata guda da ya gabata, har yanzu dubban jami’an tsaro suna cikin shiri a dukkanin sassa na birnin da kuma hanyoyin da ke isa birnin daga birane daban-daban na kasar Iraki.