Bayanin jami’an ‘yan sanda ya ce, an samu wasu kayan saddabaru da surkulle da sakandamomi a gidan matar, wadda take yaudarar mutane da yi musu rufa ido da sunan yi musu magani, ta hanyar magana da aljannu da dai sauran hanyoyi an yaudara.
Baya ga haka kuma an samu ayoyin kur’ani a cikin kayan surkullen nata, wanda aka hada su da wasu karikitai marassa kan gado, wanda hakan yake a matsayin wulakanta ayoyin kur’ani mai tsarki, kuma hakan babban laifi ne a cikin dokokin kasar Aljeriya.
Yanzu haka dai ‘yan sanda sunyi awon gaba da matar da kuma wasu daga cikin masu wurinta da sunan neman magani.
A wani labarin na daban a zantawarasa da kamfanin dillancin labaran iqna, Farfesa Richard Bensel malami a jami’ar Cornell da ke kasar Amurka ya bayyana cewa, farin jinin da Joe Biden yake da shi tsakanin Amurkawa ya ragu matuka bayan janyewa daga Afghanistan.
Ya ce matakin janyewar Amurka daga kasar Afghanistan da kuma yadda aka aiwatar da hakan cikin kankanin lokaci ya baiawa kowa mamaki a Amurka, duk da cewa Biden ya danganta hakan da matsaloli na tattalin arziki da kuma asarorin da hakan ke jawowa Amurka.
Farfesa Bensel ya ce, abin da yafi dangane da janyewar sojojin Amurka daga Afghanistan shi ne, yadda suka janye ba tare da sun yi wani shiri na taimaka ma kasar ba domin ta tsaya a kan kafafunta, ta fuskoki na tsaro da tattalin arziki da kuma kyautata rayuwar jama’ar kasar, domin kasantuwar Amurka yasa kasar a cikin manyan kalubale a dukkanin wadannan fuskoki.