A wani labarin na daban shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohammed ya sanar da cewar al’amuran tsaro sun sauya a Yankin Tillaberi inda dakarun gwamnati ke ci gaba da samun galaba akan ‘Yan ta’addan dake kai munanan hare hare.
Shugaban kasar yace yanzu ‘Yan ta’addan basa iya kaiwa sojoji hari saboda sun san abinda yake jiran su, saboda haka sun mayar da hankali akan jama’ar da basa iya kare kan su.
Bazoum ya bayyana cewar ‘Yan ta’addan na kai hari akan manoman dake aiki a gonakin su a kauyukan da suke da yakinin cewar ba zasu gamu da sojoji ba.
Wannan dai itace ziyara farko da shugaban kasar ya kai yankin Tillaberi tun bayan nasarar zaben da ya samu a watan Fabarairu, jihar da ta zama yankin zubar da jini ganin yadda ‘Yan ta’addan dake alaka da kungiyar Al Qaeda da IS ke kai munanan hare hare akan fararen hula.
Kungiyar kare hakkin Bil Adama ta Human Rights Watch tayi bayanin cewar akalla fararen hula sama da 420 ‘Yan bindigar suka akshe tsakanin watan Janairu zuwa Agustan da ya gabata.
Tunda daminar bana ta fara a watan Yuni, ‘Yan ta’addan sun mayar da hankali ne wajen kai hari akan manoman dake aiki a gonakin su.
Shugaban kasa Bazoum ya bayyana aniyar sa ta samun nasarar yaki da ‘yan ta’addan, inda yake cewa tuni suka fara ganin alamun nasarar.