Kotun Amurka ta samu wasu iyayen dilabai da suka fara gurfana kan badakalar neman gurbin shiga kwalejin Amurka da laifin bada cin hanci don shigar da ‘ya’yansu manyan jami’o’i.
Alƙalai a Boston, Massachusetts sun samu attajiri John Wilson, mai shekaru 62, da tsohon shugaban gidan caca Gamal Abdelaziz mai shekaru 64, da laifin bada cin hanci da zamba bayan shari’ar makwanni huɗu.
Akwai tsakanin wasu mutane 50 da ake tuhuma kan wannan lamari kan yadda attajiran Amurka ke amfani da kudinsu wajen samawa ‘ya’yansu manyan kwalejoji.
Wasu fitattun shirya fina-finai irinsu Lori Loughlin da Felicity Huffman sun kasance manyan fitattun mutane da suka fuskanci hukunci a gagarumin shari’ar badakalar da akayiwa lakabi da “Operation Varsity Blues.”
‘Yar wasan “Full House” Loughlin ta yi zaman gidan yari na watanni biyu a bara bayan da ita da mijinta suka yarda sun biya $ 500,000 don samun gurbin shigar’ daya’yansu mata biyu a Jami’ar Kudancin California.
A wani labari na daban wata kotu a Amurka ta yanke hukuncin daurin shekaru 10 kan fitaccen attajirin Najeriya Obinwanne Okeke saboda samun sa dalaifin almundahana da ta shafi miliyoyin daloli.
Kotun tace Okeke ta hanyar badda kama yayi ta amfani da kafar intanet yana kutse asusun ajiyar jama’a da kamfanoni wajen kwashe wadannan kudade.
Mai rike da kujerar Babban lauyan gwamnatin Amurka a Gabashin Virginia Raj Parekh ya bayyana hukuncin a matsayin wanda ya tabbatar da kokarin hukumomi irin su EDVA da FBI na zakulo masu aikata laifi wajen cutar Amurkawa daga kowanne sako na duniya domin ganin an hukunta su.
Takardun kotun sun ce Okeke mai shekaru 33 ya tafiyar da wasu kamfanonin da aka kira Invictus a Najeriya da kuma wasu kasashen Afirka, kuma tsakanin shekarar 2015 zuwa 2019 yayi amfani da damar sa wajen aikata laifuffuka ta hanyar intanet.
Kafin ya fada hannun jami’an tsaron FBI a shekarar 2019, Okeke ya shiga cikin matasan attajiran da mujallar Forbes ta bayyana da suka yi suna wajen zuba jari a Afirka.