Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Ukraine ta ce, sama damutane 351 ne suka rasa rayukansu, ciki har da kananan yara 14 tun bayan da Rasha ta kutsa cikin kasar a makon da ya gabata.
Wannan dai ya faru ne tun bayan ranar 24 ga watan Fabrairu, lokacin da shugaban Rasha ya sanar da kutsawar sojojinsa Ukraine, yana mai cewa Rasha za ta raunata karfin sojin Ukraine kadai ba tare da yiwa fararen hula illa ba.
Sai dai kuma a hotuna da faya-fayan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta na nuna yadda sojojin Rasha ke jefa makamai kan gine-ginen da suke da tabbacin akwai farafen hula a ciki, lamarin da ke sanadiyyar mutuwarsu, abin da tuni hukumomin Rasha suka musanta suna masu kwatanta hakan da farfagandar turawan yamma.
Tuni dai dukannin kasashen biyu suka tabbatar da cewa dakarun su sun hallaka a gwabzawar da ake yi, amma dai babu wacce ta bada adadin sojojin da suka mutu din.
A wani labarin na daban Dan wasan tsakiya na Tottenham, Dele Alli yace tsohon kocinsa Jose Mourinho ya cika mayar da hankali a kan abokan hamayya a yayin shirye shiryen tinkarar wasa.
Sai dai yanzu dan wasan ya zama mai murza leda a kullayaumin a karkashin mai horarwa, However, Nuno Espirito Santo.
Dan shekara 25 din kasance cikin ‘yan wasan tsakiya da ake damawa da su a tsakiyar filin Tottenham a wannan zamani na Koch Nuno, kuma ya buga ilahirin wasannin gasar Firimiyar Ingila na wannan kaka tun da aka fara.
Alli ya shaida wa manema labarai cewa Mourinho yana da dabi’ar daukar lokaci yana nazari a kan abokan hamayya, maimakon ya mayar da hankali a kan abin da ya dace a yi.