Binciken kwamitin ya gano cewa akwai tsakanin fada-fada masu lalata da yara kimanin sama da 2,900 zuwa sama da 3,200 ko wasu membobin cocin da suka aiki a wancan lokaci.
A ranar Talata ne ya kamata a fitar da rahoton bayan bincike na shekaru biyu da rabi da aka yi bisa kundin bayanan mujami’ar da kotu da kuma na ‘yan sanda, haka zalika da kuma hirarraki da shaidu.
A bangaren su shugabannin Darikar Katolika a kasar Faransa sun nemi gafarar mutanen da aka ci zarafinsu sakamakon wasu bayanan fallasar da ya nuna cewar limaman cocin sun dade suna lalata da kananan yara.
Wannan shi ne labari mafi muni da ya shafi cocin tun shekarar 2011 lokacin da aka dakatar da wani Bishop watanni uku saboda ya ki fallasa irin wannan labari.
Rahotanni sun ce akwai sakwannin imel sama da 100 da cocin ta samu a tsawon watanni shida da ke bayani akan lalata da yara tun a 1960.
Shugaban darikar da ke Paris, Andre Vingt-Trois ya shaidawa mabiyansa cewar cocin ta gaza wajen kare yaran.