Sama da kashi 56% na turawa suna bakin cikin dawowar Trump.
A sakamakon Wani bincike da wata fitacciyar cibiyar bincike ta Turai ta gudanar, yana nuni da cewa rabin al’ummar wannan nahiya suna bakin cikin dawowar Trump a matsayin shugaban kasar Amuruka.
Sama da rabin turawa ne ke ganin komawar Trum White House a matsayin shugaban kasa wata babbar barazana ce ga kasar ta amuruka. Sama da Kashi 56% na mahalarta taron “Majalisar Turai kan Harkokin Waje” sun bayyana hakan.
domin ganin labarai na gaba ku danna link din kasa..👇
Hedkwatar wannan cibiyar tana birnin Berlin na Jamus, kuma tana da ofisoshi a Ingila, Spain, Faransa, Italiya, Bulgaria da Poland. kuma a kwanan nan ne ta buga sakamakon binciken da ta yi kan ra’ayin mutanen Turai game da yakin Ukraine. .
Sakamakon ya nuna cewa kashi 27% a kasashe 12 na nahiyar turai ne kawai suke farin cikin dawowar Trump,
Wanda kashi 57% sunyi nuni da cewa babban hatsari ne Trump ya dawo shugaban kasa.
A sakamakon da wannan cibiyar ta fitar tayi nuni da cewa bayan tambayar da suka yiwa al ummar turai kan cewa ya suke gani idan Amurka ta dakatar da taimakon da takeyi ga kasar Ukrine.
Kashi 41% na wannan al’ummar sun yi nuni da cewa a wannan halin idan har Amurka ta dakatar da tallafin da take kaiwa ga Ukrine sedai EU ta kara tallafin da take kaiwa Ukrine din,
Amma sama da kashi 33% sun yi nuni da cewa ya kamata EU ta dakatar da nata tallafin da take kaiwa Ukrine.