A wannan satin ne Jagoran juyin juya halin musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamene’i ya aike da sakon ga matasa wanda akasari ‘yan jami’a ne a wani kokari na jinjina musu dangane da nuna goyon bayan su ga al’ummar falasdinawa wadanda Isra’ila take ta kashewa.
A sakon na Jagoran ya bayyana matasan Amurkan a matsayin wani bangare na fafutukar gwagwarmayar neman ‘yancin raunana duk da matsin lambar da suke fuskanta daga gwamnatin su.
Jagoran ya bayyana hadafin gwagwarmaya shine dakatar da zalunci kamar dai zaluncin Isra’ila.
Yanzu kasar Isra’ila tana cigaba da zaluncin ta ba daga Kafa, kamar yadda Jagoran ya bayyana a sakon masa.
Jagoran ya bayyana cewa, falasdinu kasa ce mai zaman kanta wacce take da ‘yan kasa wadanda suka hada da musulmi, kiristoci da kuma yahudawa kuma kasa ce mai dadadden tarihi amma bayan yakin duniya da taimakon Ingila aka shigar da dubunnan ‘yan tada zaune tsaye yankin suka shiga garuruwan mutane, suka kashe da dama tare da rushe gidaje da kasuwanni suka fitar da mutane daga gidajen su sa’annan suka kafa kasa mai suna Isra’ila a kasar kwace, kamar yadda Jagoran ya bayyana a sakon nasa.
Jagoran kuma ya bayyana Amurka da Ingila a matsayin manyan masu taimakon Isra’ila, inda suke taimaka mata a fannin, siyasa, tattalin arziki da kuma makamai.
Jagoran ya bayyana cewa Amurka bata taba nuna damuwa kan laifikan Isra’ila ba, inda ya bayyana cewa ko yanzu da wasu bayanan nuna damuwa da gwamnatin Amurkan ta iya yi matsayin riya.
A karshe Jagoran ya bayyana cewa, “Ni inason na tabbatar muku da cewa yanzu yanayi yana canjawa ne”
A karshe Jagoran ya bukaci matasan da su dingi karanta Al’qurani saboda muhimmin sakon da yake dauke da shi.
Rahotanni dai sun tabbatar da cewa sakon Jagoran ya isa ga matasan kuma sun cigaba da fafutukar gwagwarmayar su kamar yadda ya bukata.